Mark 15

Yesu a Gaban Bilatus

1Da sassafe, sai manyan firistoci tare da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka ɗaure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.

2Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”

Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

3Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. 4Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”

5Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.

6Yanzu fa, alʼada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa. 7Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ʼyan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. 8Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yǎ yi musu abin da ya saba yi.

9Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 10Don ya san saboda kishi ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi. 11Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

12Bilatus ya tambaye su, ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”

13Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

14Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”

Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”

15Don son yǎ faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.

Sojoji Sun Yi wa Yesu Baʼa

16Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. 17Suka sa masa wata riga mai launin shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. 18Sai suka fara ce masa, “Ranka yǎ daɗe sarkin Yahudawa!” 19Suka dinga bugunsa a ka da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa ban girma na baʼa. 20Bayan da suka gama yin masa baʼa, suka tuɓe rigar mai launin shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.

Gicciyewa

21Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yǎ ɗauki gicciyen. 22Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai.) 23Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yǎ rage zafi, amma bai sha ba. 24Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuriʼa a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

25Saʼa ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 26Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, “SARKIN YAHUDAWA.” 27Suka gicciye ʼyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
Waɗansu rubuce rubucen hannu hagu, 28 aka kuma cika nassi wanda ya ce, “Aka lissafta shi tare da masu laifi” (Ish 53.12)
28
This verse is empty in this translation.
29Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

31Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa baʼa a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! 32Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Israʼila, yǎ sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

Mutuwar Yesu

33Daga saʼa ta shida har zuwa saʼa ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34A daidai saʼa ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” Wanda yake nufin, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”
Zab 22.1


35Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Eliya.”

36Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yǎ sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Eliya zai zo yǎ saukar da shi.”

37Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.

38Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. 39Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”

40Waɗansu mata suna ƙallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yosi, da kuma Salome. 41A Galili waɗannan mata ne suka riƙa binsa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.

Janaʼizar Yesu

42Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye, (wato, ana washegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai 43Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. 45Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin. 46Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, saʼan nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin. 47Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yosi sun ga inda aka kwantar da shi.

Copyright information for HauSRK